Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar peninsula ta kasar Qatar ta habarta cewa, Ridawan Alfakhir masanin taurarin nan na kasar Canada kuma daya daga cikin fitattun musulmin kasar ya bayyana cewa a cikin shekara ta 2013 za a kafa wata tasha a kan kwallon wata mai suna Muhammad (SAW) Ridawan wanda masani ne kan harkokin sararin samaniya da taurari, mamba ne a cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Canada, wanda ya bayyana cewa manufarsa ta yin hakan ita ce tabbatarwa duniya cewa musulmi suna da samuwa a dukkanin bangarori na ilimi. 603108