Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar haddaiyar daular larabawa WAM an habarta cewa, an fitar da nushar kur'ani ta farko da aka tarjama a cikin harshen Ukraine wanda wani malalin jami'a musulmi a kasar ya gudanar bayan kwashe tsawon shekaru. Bayanin ya kara da cewa bayan tarjama ayoyin kur'ani daga farkonsa har zuwa karshe, an kuma tarjama wasu kalmomi tare da yin Karin bayani kan ma'anoninsu. 603047