IQNA

Taro Kan Halin Da Ake Ciki A Yankin Gaza A Kasar Faransa

10:00 - June 24, 2010
Lambar Labari: 1945632
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zama a kasar faransa domin yin dubi kan littafin da Karim Labhur wani marubuci ya wallafa kan halin da ake cikin a yankin zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin yanar gizo na saphirnews cewa, za a gudanar da wani zama a kasar faransa domin yin dubi kan littafin da Karim Labhur wani marubuci ya wallafa kan halin da ake cikin a yankin zirin Gaza. Bayanin ya kara da cewa a cikin littafin, marubucin ya bayyana zirin Gaza a matsayin wani makeken kurkuku da sama da mutane miliyan daya da rabi suke rayuwa a cikinsa, sakamakon killace yankin baki daya da haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da yi tsawon shekaru uku, ba tare da masu rajin kare hakkin dank o raya dimokradiyya sun tabuka komai ba. 602898



captcha