Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shugaban hadakar kwamitocin majalisar shawarar Musulunci ta Iran Hassan Malik Muhammadi ya bayyana cewa, wilayar Imam Ali (AS) alama ce ta kamalar imani da Allah madaukakin sarki, kuma ita ce sahihiyar hanyar biyayya ga manzon Allah (SAW) da aikata umurnin ranar gadir. Malamin ya ci gaba da cewa Imam Ali (AS) shi ne mai shiryar da al'ummar manzo a bayansa, kauce ma tafarkinsa yin watsi ne da sahihin tafarkin manzo.603389