IQNA

Gasar Kasa Da Kasa ta Dubai Karo Na Hudu

15:48 - June 24, 2010
Lambar Labari: 1945772
Bangaren kasa da kasa; Ibrahim Muhammad Bumalha shugaban komitin shirya gasar kasa da kasa ta kur'ani a Dubai ya bada labarin fara babban gasar Dubai karo na hudu a watan Azumin Ramadan.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga kamfanin dillancin labarai na hadeddiyar daular Larabawa Wam ta watsa labarai cewa; Ibrahim Muhammad Bumalha shugaban komitin shirya gasar kasa da kasa ta kur'ani a Dubai ya bada labarin fara babban gasar Dubai karo na hudu a watan Azumin Ramadan. Ya kara da cewa; dukan mambobin komitin zartarwa sun shirya domin gudanar da wannan gasar kuma a dabra da wannan gasar za a gudanar da jawabai da sauran shirye-shirye masu kayatarwa.


603471

captcha