Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga bangaren hulda da jama'a ta cibiyar Musulunci a Britaniya ta watsa rahoton cewa; : mahalanta taron na kasa da kasa na malamai da masana na duniyar musulmi da suke yin nazari da bincike kan al'ummar musulmi a London da kuma larurar karfafa rawar da wannan cibiya ke gudanarwa ta fuskar hada kawunan musulmin duniya. A karshen taron an fitar da wata sanarwar bayan taron da a cikinta aka bayyana bukatar kara kusanci a aikace da wajen yada addini ta fuskar hadin kan musulmi da kuma amfani da duk wata hanya da za ta tabbatar da hakan.
603438