Bangaren ilmi da nazari: a kasar Zimbabwe za a gudanar da wani taro mai taken rawar da imam Ali (AS) ta taka a tarihin Musulunci kuma wanna taro za a gudanar da shi ne a daidai ranar tunawa da zagayowar irin wannan rana ta haifuwar Imam Ali (AS) kuma za a gudanar da wannan taro a birnin Harari fadar mulkin kasar Zimbabwe.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta dake hukumar kula da al'adun jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma kusanci a tsakanin kasashen musulmi da musulmi ta watsa rahoton cewa; a kasar Zimbabwe za a gudanar da wani taro mai taken rawar da imam Ali (AS) ta taka a tarihin Musulunci kuma wanna taro za a gudanar da shi ne a daidai ranar tunawa da zagayowar irin wannan rana ta haifuwar Imam Ali (AS) kuma za a gudanar da wannan taro a birnin Harari fadar mulkin kasar Zimbabwe. Wannan taro za a gudanar da shi ne karkashin kulawar ofishin yada al'adun Iran a kasar Zimbabwe daga ranar hudu zuwa shidda ga watan Tir.
603294