IQNA

Za A Samar Da Kudaden Musulunci A Kasar Indonesia

18:43 - June 24, 2010
Lambar Labari: 1945819
Bangaren kasa da kasa; Za a samar da wasu takardun kudade na Musulunci a kasar Indonesia domin yin amfani da su a harkokin kasuwanci da bankunan muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ministan harkokin kasuwancin kasar Indonesia ya sanar cewa, za a samar da wasu takardun kudade na Musulunci a kasar Indonesia domin yin amfani da su a harkokin kasuwanci da bankunan muslunci. Bayanin ya ci gaba da cewa kudin da za a samar za su kimar dalar Amurka miliyan dari biyar zuwa miliyan dari shida, kuma da sannu za a fara rarraba su a dukkanin bankunan Musulunci da ke cikin kasashen musulmi domin yin amfani da su a matsayi na kasa da kasa. 603413



captcha