IQNA

Yada Ilmi Shi Ne Babbar Hanyar Cin Nasarar Yakin Ruwan Sanyi

Bangaren al'adu da fasaha; Samar da hanyoyi na yada ilimi a cikin kasashen musulmi ita ce hanyar da tafi dacewa domin kalubalantar yakin ruwan sanyi da ake yi kan musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da bangaren yada labaransa na birnin Qom ya yabar an habarta cewa, daraktan cibiyar yada al'adu da ilimi ta kasa da kasa Habib Kahrimani ya bayyana cewa, samar da hanyoyi na yada ilimi a cikin kasashen musulmi ita ce hanyar da tafi dacewa domin kalubalantar hanyoyin yakin ruwan sanyi da ake yi kan musulmi. Ya ci gaba da cewa hanyoyin yada ilimi suna da yawa musamamn ma a wannan zamani da kayyaki suke da sauki, kama daga hanyoyin yanar gizo har zuwa littafai da za a iya karantawa. 603528