Bangaren fikira da ilimi; Za a fara gudanar da wani shiri na horar da dalibai masu isar da sakon addini a kasar Kenya, wanda karamin ofishin jakadancin Iran ya shirya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da jama'a da yada labarai na cibiyar yada al'adu da ilmomin Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa, za a fara gudanar da wani shiri na horar da dalibai masu isar da sakon addini a kasar Kenya, wanda karamin ofishin jakadancin Iran a kasar ya shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan bayar da horo zai hada ne da dalibai masu karatu a cibiyoyin ilmi na mazhabar iyalan gidan manzon Allah, da sauran masu samun horo wannan ofishin jakadancin. 603614