Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin yanar gizo na mosquefoundation an bayyana cewa, ana shirin gudanar da wata gasar harder kur'ani mai tsarki a jahar Ilinews ta kasar Amurka, wadda musulmi mazauna jahar za su gudanar a cikin watan Ramadan. Bayanin ya ci gaba da cewa an kasa yadda za a gudanar da hardar tsakanin 'yan shekaru hudu zuwa bakwai, da kuma da kuma 'yan shekaru takwas zuwa sha daya, sai kuma sha biyu zuwa sha biyar.603571