Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatollah Sayyid Khamenei jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, dukkanin al'ummar da ta yi imani da yin riko da koyarwar kura'ni tana makoma mai kyau. Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin da wasu daga cikin daliban jami'a suka kai masa ziyara daga cikin sojojin sa kai da aka fi sani da Basij. Inda ya jadda musu irin muhimmancin da ke tatatre da yin aiki da koyarwar kur'ani mai tsarki tsakanin al'umma, da yadda hakan kan yi tasiri wajen shiriyar mutane da dama. Ya ce yin aiki da koyarwar kur'ani kan mayar da zuciyar mutum ba ya tsoron kowa sai ubangiji mahaliccinsa, kuma hakan na bakanta wa manyan kasashe masu girman kai, domin kuwa su kur'ani shi ne babban abokin adawarsu. 603643