Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa FKM an habarta cewa, an fara gudanar da zaman taro na kas ada kasa kan kur'ani da hakkokin ilimi a cibiyar raya al'adu da addini ta Furat da ke birnin Ostanbul na kasar Turkiya. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da zaman taron ita ce raya tattaynawa kan harkokin ilimi da suka danganci addini da kuma kur'ani mai tsarki. 604011