Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wanda ya jagoranci sallar juma'a a birnin Tehran Hujjatul Islam Kazim Sadiqi ya bayyana cewa takunkumin majalisar dinkin duniya kan Iran ba sabon lamari ba ne, kuma al'ummar da ta dogara da Allah bat a shayin a kakaba mata takunkumi saboda riko da gaskiya. Malamin ya ci gaba da cewa a koda yaushe kasashe masu girman kai suna fatan ganin sun bautar da sauran kasashe musamamn ma masu tasowa, wanda kuma Iran tuni ta kama hanyar zama 'yantatta daga zalunci da danniyar wadannan kasashe.603985