Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na Balkan an habarta cewa, an gudanar da zaman taro da ya yi dubi kan horas da malaman addinin Musulunci da kuma limamai na kasar Crotia a birnin Zakab fadar mulkin kasar. Wannan zaman taro shi ne karo na goma da ake gudanar da irinsa a kasar, domin tabbatar da cewa jagororin musulmin kasar suna gudanar da ayyukansu ba tare da fuskantar wata matsala ba. 604010