IQNA

Yeman Za Ta Dauki Bakuncin Taron Harkokin Bankin Musulunci

Bangaren al'adu da fasaha; A zaman da wakilan kasashe mambobi a babban bankin Musulunci suka gudanar a kasar Azarbaijan, an zabi Yeman ta zama mai saukin taron a shekara mai zuwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada labaransa na birnin Baku a kasar Azarbaijan ya habarta cewa, a zaman da wakilan kasashe mambobi a babban bankin Musulunci suka gudanar a kasar Azarbaijan, an zabi Yeman ta zama mai saukin taron a shekara mai zuwa. Bayanin ya ci gaba da cewa zaman taro ya yi dubi ne kan muhimman batutuwa da suka danganci harkokin kudi a kasashen musulmi, musamman ma mambobi a bankin bunkasa harkokin tattalin arzikin Musulunci, kuma kasar Yeman ce za ta dauki nauyin bakuncin taron da za a gudanar a shekara mai zuwa. Wannan dai shi ne karo na talatin da biyar da ake gudanar da zaman. 604008