Bangaren al'adu da fasaha; An yi kira ga limaman Juma'a da su mayar da hankali wajen yin hannuka mai sanda kan kyawawan dabi'u a cikin hudubobinsu na juma'a a kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Bangaren yada labaransa na birnin Beirut na kasar Labanan ya habarta cewa, An yi kira ga limaman Juma'a da su mayar da hankali wajen yin hannuka mai sanda kan kyawawan dabi'u a cikin hudubobinsu na juma'a a kasashen musulmi. Shugaban cibiyar kula da harkokin Musulunci ta yankin Tripoli na kasar Labanan din Hussam Sibat shi ne ya yi wannan kira. Inda ya bayyana cewa babban abin da matasa suke bukata shi ne shiryarwa zuwa ga koyarwar Musulunci maimakon koyi da rayuwar turawa.604002