Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, majalisar malaman addinin msuulunci ta kasar ta fitar da wani bayani da ke cewa, babbar majalisar malaman addinin Musulunci ta kasar Rasha na yin kira ga malaman addinin Musulunci na kasar Kyrgystan ta su yi sulhu tsakanin al'ummar kasar. Daya daga cikin malaman addinin Musulunci a kasar Kyrgystan ya bayyana hakan da cewa mataki mai kyau domin kawo karshen rikicin da ya barke a kasar, tsakanin 'yan kabilar Kyrgys da kuma 'yan Uzbik. 603642