IQNA

Gasa Kan Sirar Sayyida Zahra (AS) A Birnin Beirut

Bangaren al'adu da fasaha; An gudanar da gasar sirar sayyida Zahra(AS) a birnin Beirut na kasar Labanan, wadda ta samu halartar yara 'yan makaranta daga bangaren kungiyar hizbullah.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga reshensa birnin Beirut na kasar Labanan an habarta cewa, An gudanar da gasar sirar sayyida Zahra(AS) a birnin Beirut na kasar Labanan, wadda ta samu halartar yara 'yan makaranta daga bangaren kungiyar hizbullah. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taron na daya daga cikin tarukan da bangaren mata na kungiyar ke shiryawa a duk shekra. 603997