Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga cibiyar sadarwa ta yanar gizo ta albalagh an bayyana cewa, an bude wata cibiyar kur'ani mai tsarki a birnin Najaful ashraf a kasar Iraki, wadda aka bai wa suna cibiyar hardar kur'ani ta Alanwar. Wannan cibiyar za ta mayar da hankali wajen yada ilmomin kur'ani, da hakan ya hada koyar da karatunsa, koyar da hardarsa da kuma ilmomin ka'idojinsa, kuma nan bad a jimawa za a fara gudanar da ayyuka a cikin wannan cibiya. 603596