Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, An fara gudanar da wata gasa ta kur'ani mai tsarki tare da bayar da horo kan ilmin tajwidi a babbar cibiyar kur'ani darul kur'an ta Imam Khomeni (RA) da ke birnin Arak. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da shirin bayar da horon ita ce karfafa matasa wajen bayar da himma da maida hankali kan harkokin kur'ani. Bude taron ya samu halar makarnta da ma wasu daga cikin jami'an gwamnati a yankin. 602814