Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da tarukan maulidin Imam Ali(AS) a masallatai kimanin 220 da wasu wuraren taru 44 a cikin birnin Tehran a daren jiya. Bayanin ya ci gaba da cewa a wurin tarukan malamai sun gabatar da jawabai daban-daban, tare da yin hannuka mai sanda ga jama'a kan su yi koyi da Amirul muminin acikin dukkanin lamurransa, wanda hakan shi ne kawai hanyar tsirar al'umma, kuma ta hanyar yin hakan ne za ta yi koyi da hakikanin koyarwar manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka. 603050