IQNA

Aiki Tare Tsakanin Jami'o'in Musulmi Na Malaishiya da Saudiya

Bangaren kasa da kasa; karkashin wata sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin jami'ar Taiba ta Saudiya da jami'ar ilmomin addinin Musulunci ta Malaishiya bangarorin biyu sun aminci da su yi aiki tare ta fuskar bincike da nazari na addini da hadisan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi .
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshebta da ke kudu maso gabacin Asiya bayan ta nakalto daga jaridar Alhayat ta kasar Saudiya ta watsa rahoton cewa; karkashin wata sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin jami'ar Taiba ta Saudiya da jami'ar ilmomin addinin Musulunci ta Malaishiya bangarorin biyu sun aminci da su yi aiki tare ta fuskar bincike da nazari na addini da hadisan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi . Wannan mataki wani mataki ne da zai taimakawa jami;o'in da kuma za zama a bin koyi ga sauran jami'oi na kasashen musulmi da za su iya aiki a tsakaninsu domin ciyar da al'ummmominsu gaba da fadakar da su da kuma bangaren ili da zamantakewa.


604209