IQNA

OIC Tana Nuna Damuwarta Kan Rikicin Kasar Kyrgystan

19:37 - June 27, 2010
Lambar Labari: 1946897
Bangaren siyasa da zamantakewa; Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta oic ya fitar da wani bayani don nuna damuwa kan rikicin da ya faru a kasar Kyrgystan.
Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da bangaren yada labarai na kasar Kyrgystan ya bayar an habarta cewa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta oic Abdullah Alturki ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya nuna damuwa kan rikicin da ya faru a kasar Kyrgystan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu biyu, wasu dubbai kuma suka jikkata, yayin wasu sama da dubu dari daya daya suka shiga gudun hijira. 604012



captcha