IQNA

Tasirin Ilmomin Kur'ani Da Hadisi A kwalwar Matasa

Bangaren fikira da ilmi; Bayar da ilimin kur'ani mai tsarki da hadisan ma'aiki da na limaman gidan manzon Allah na da gagarumin tasiri a cikin rayuwar matasa musulmi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a tarukan bayar da horo ga matasa na lokutan bazara da ake gudanarwa a sassa daban-daban na kasar Iran an jadda cewa, bayar da ilimin kur'ani mai tsarki da hadisan ma'aiki da na limaman gidan manzon Allah na da gagarumin tasiri a cikin rayuwar matasa musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tsarin bayar da horo ya kan kunshi bangarori na ilmin kur'ani, akida, fikihu, hadisi, zamantakewa, al'adu adabi da dai sauransu. 604139