IQNA

Shahadar Beheshti Ta Raya Juyin Juya Halin Musulunci

19:30 - June 27, 2010
Lambar Labari: 1946904
Bangaren siyasa; Shahadar da Ayatollah Sayyid Hussain Beheshti ya yi ta taimaka wajen ruhin juyin juya halin Musulunci a cikin kasar Iran da ma wajen kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wakilin jagoran juyin juya hali a yankin Azarbaijan ta gabas ya bayyana cewa, shahadar da Ayatollah Sayyid Hussain Beheshti ya yi ta taimaka wajen ruhin juyin juya halin Musulunci a cikin kasar Iran da ma wajen kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa shahid Beheshti ya sadaukantar da rayuwarsa domin addininsa da al'ummarsa, ya taka gagarumar rawa wajen samun nasarar juyin juya halin Musulunci, wanda shadarsa sai ta zama wani mabudi na raya ruhin juyin a cikin zukatan al'umma. 604153



captcha