IQNA

Ma'anonin Kur'ani Suna Yin Tasiri Wajen Samar Da Natsuwa

19:30 - June 27, 2010
Lambar Labari: 1946905
Bangaren siyasa da zamantakewa; Fahimtar ma'anonin kur'ani mai tsarki na da gagarumin tasiri wajen samar da natsuwa a cikin rayuwar mutum.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban darakta mai kula da harkokin sadarwa da hulda da jama'a a cibiyar kula da al'adu ta lardin Azarbaijan ya bayyana cewa, Fahimtar ma'anonin kur'ani mai tsarki na da gagarumin tasiri wajen samar da natsuwa a cikin rayuwar mutum, tare da yi masa jagora a cikin dukkanin lamurran rayuwarsa. Bayanin ay ci gaba da cewa, gudanar da taruka ake yi kan kur'ani da kuma gabatar da jawabai kan ma'anonin ayoyin kur'ani da hikimomin da ke tattare a cikinsu, suna taimaka wa matuka.604026



captcha