Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran samanhaber an bayyana cewa, an fara gudanar da wata gasar limancin salla a tsakanin matasa a gidan talabijin din kasar Malazia, inda ake saka matasa su jagoranci salla tsakanin takwarorinsa. Bayanin ya ci gaba da cewa gasar tana da tasiri matuka wajen zaburar da matasa domin kula da ayyukan ibada, musamman ma salloli. 604116