IQNA

Yada Musulunci Da Kiyaye Shi Ita Ce Babbar Manufar Imam (AS)

19:28 - June 27, 2010
Lambar Labari: 1946910
Bangaren siyasa da zamantakewa; Yada addinin Musulunci a cikin al'ummomi da kuma kiyaye ka'idojinsa da taimakon mai rauni da tabbatar da adalci ita ce babbar manufar Imam Ali (AS)
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daya daga cikin malaman addinin Musulunci a yankin Kerman Mahdi Arabpor ya bayyana cewa, yada addinin Musulunci a cikin al'ummomi da kuma kiyaye ka'idojinsa tare da taimakon mai rauni da tabbatar da adalci tsakanin bayin Allah ita ce babbar manufar Imam Ali (AS) malamin ya ci gaba da cewa da a ce duniya ta bi tafarkin Imam Ali (AS) da ta zauna lafiya, da ta rayu cikin salama da samun yardar ubangiji. 604036




captcha