IQNA

Babban Muftin Sabiya Ya Yi Allah Wadai Da Takwalar Da Ake Yi Musulunci

10:26 - June 28, 2010
Lambar Labari: 1947128
Bangaren kasa da kasa: babban mai bada fatawa a kasar Sabiya ya yi nuni da tsananin matakai na cin fuska da takwalar da ake nunwa musulmi da addinin Musulunci da kuma nunawa musulmi wariya a Sabiya a tsakanin al'ummar wannan kasa ya yi Allah wadai da wannan hali da wani gungu a wannan kasar ke yi.


Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta da ke yankin Balkan bayan ta nakalto daga jaridar Faramrazi a yankin gabas ta tsakiya ta watsa rahoton cewa; babban mai bada fatawa a kasar Sabiya ya yi nuni da tsananin matakai na cin fuska da takwalar da ake nunwa musulmi da addinin Musulunci da kuma nunawa musulmi wariya a Sabiya a tsakanin al'ummar wannan kasa ya yi Allah wadai da wannan hali da wani gungu a wannan kasar ke yi. Mua'ammar Zukarlic babban mai fitar da fatawa a kasar ta Sabiya kuma shugaban latijawan kasar a ranar biyar ga watan Tir na wannan shekara ta hijira shamsiya ya bayyana Allah wadansa.


604889
captcha