IQNA

An Rufe Wasu Shafuka 17 Na Yanar Gizo A Kasar Pakistan

15:30 - June 28, 2010
Lambar Labari: 1947532
Bangaren kasa da kasa; An rufe wasu shafukan sadarwa na yanar gizo guda 17 a kasar Pakistan saboda yada abubuwa da suka saba wa musulunci da suke yi karkashin yahoo da kuma google.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo topnews an bayyana cewa, a kasar pakisan an rufe wasu shafukan sadarwa na yanar gizo guda 17 Pakistan saboda yada abubuwa da suka saba wa musulunci da suke yi karkashin yahoo da kuma google. Bayanin ya ci gaba da cewa kakakin ma'aikatar kula da harkokin al'adu na kasar ne ya sanar da hakan, inda ya tabbatar da cewa an dauki matakin ne domin taka musu birki kana bin da suke yin a bata sunan addinin musulunci. 604698



captcha