IQNA

An Fara Zaman Taro Na Dangantakar Addinai A Belgium

15:32 - June 28, 2010
Lambar Labari: 1947533
Bangaren kasa d akasa; An fara gudanar da wani zaman taro a matsayi na kasa da kasa a birnin Brussel na kasar Belgium da nufin kara kusanto da fahimtar juna tsakanin addinai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar ISESCO an bayyana cewa, an fara gudanar da wani zaman taro a matsayi na kasa da kasa a birnin Brussel na kasar Belgium da nufin kara kusanto da fahimtar juna tsakanin addinai. Bayanin ya ci gaba da cewa kungiyar ISESCO din ce ta dauki nauyin kiran zaman taron, wanda ke samun halartar masana daga daga kasashen turai da kuma na musulmi gami da wasu kasashen nahiyar Asia. 604576



captcha