IQNA

An Girmama Wasu Sojoji Da Suka Lashe Gasar Kur'ani A Kuwait

15:31 - June 28, 2010
Lambar Labari: 1947535
Bangaren kasa da kasa; An girmama wasu sojoji da suka lashe wata gasar kur'ani da aka shiryawa jami'an tsaro a kasar Kuwait, wadda aka gudanar a karo na bakawai a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wano rahoto daga jaridar kasar Kuwait alra'ayi cewa, an girmama wasu sojoji da suka lashe wata gasar kur'ani da aka shiryawa jami'an tsaro a kasar Kuwait, wadda aka gudanar a karo na bakawai a fadar mulkin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar ita ce ta dauki nauyin shirya gudanar da wannan gasa. Daga cikin wadanda suka halarci gasar hard a 'ya'yan wasu daga cikin jami'an tsaron kasar. 604621



captcha