Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo thenrwa an bayyana cewa, An gudanar da wani zaman taro a birnin Karachi an kasar Pakistan kan makomar tattalin arzikin kasashen musulmi, wanda cibiyar kula da harkokin kudi da kasuwanci ta kasar ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi, da kuma wasu daga cikin malaman jami'oin kasar. 604473