Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A wata zantawa da ta hada bangaren labaran da wani masani kuma makarancin kur'ani na kasa da kasa Mahdi Dagale ya bayyana cewa, addu'ar sabah ta Amirul muminin tana tattare da wasu abubuwa na musamman da suka hada da balaga da kuma hikima wajen kaskantar da kai ga Allah madaukakin sarki. Malamin ya ci gaba da cewa wannan addu'a tana tattare da wani sirri wanda Allah ne kawai ya san sa sai kuma bayinsa da ya sanar a cikin ikonsa.591066