Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalato daga jaridar nan ta Al-riyad an bayyana cewa, an tarjama karlmomin kur'ani mai tsarki ta hanyar digital a cikin harshen turancin ingilishi, wanda wani masani musulmi dan kasar Birtaniya mazaunin birnin London ya yi. Bayanin ya ci gaba da cewa za a iya yin amfani da wannan sabuwar hanyar domin gano tarjamar kowace kalma daga cikin kalmomin kur'ani daga harshen larabci zuwa turanci cikin sauki. 604922