Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar nan da ake bugawa a kasar Masar yau sabi an bayyana cewa, daya daga cikin malaman addinin Musulunci a kasar Sudan kuma tsohon shugaban nkasar Sudan Sadiq almahdi ya bayyana cewa, wuce gona da iri shi ne babban ummul haba'isin jawo rarraba tsakanin al'ummar musulmi, tare da mayar da wani bangare ba kan sahihiyar akida ta Musulunci ba. Ya ce da kowane bangaren musulmi zai girmama daya bangare da ba a samu sabani mai tsanani ba.604965