Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren hulda da jama yada labarai na cibiyar kusanto da fahimtar juna tsakanin mazhabobin Musulunci cewa, babban sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci Ayatollah Tskhiri ya bayyana cewa, tattaunawa tsakanin addinai lamari ne da ya zama wajibi. Bayanin ya ci gaba da cewa samun fahimtar juna tsakanin dukkanin addinai shi ne zai bayar da dama a warware abubuwan da ake da sabani a kansu, ba tare da kowane bangare ya bar akidarsa ba. 604903