Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nasij an bayyana cewa, za a fara gudanar da wani shiri na bayar da horon hardar kur'ani mai tsarki a masallacin birnin Dammam da ke gabacin kasar Saudiyya a karo na takwas. Rahoton ya ce shirin za a gudanar da shi na kankanin lokaci, day a kebanci bazara kawai, kafin yara su kammala hutu su koma makarantunsu. 605445