Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na islamawareness an habarta cewa, daga ranakun sha daya zuwa sha bakwai ga watan gobe ne za a gudanar da wani taro da aka baiwa taken makon masaniya dangane da addinin musulunci a Newzeland. Taron zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar, gami da wakilan ciboyi na musulmi da ma wadanda ba na musulmi ba, inda za a gabatar da laccoci dangane da addinin musulunci da manufofinsa da kuma koyarwarsa. 605401