IQNA

Gasar Hardar Kur'ani Mai Tsarki A Fadin Kasar Birtaniya

15:10 - June 29, 2010
Lambar Labari: 1948287
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki da za ta hada dukkanin yankunan Birtaniya, wadda cibiyar kula da harkokin musulunci right start ta shirya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na rightstart an bayyana cewa, ana shirye-shiryen gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki da za ta hada dukkanin yankunan kasar Birtaniya, wadda cibiyar kula da harkokin musulunci right start ta kasar ta shirya gudanarwa. Kungiyoyi daban-daban na musulmi da suke garuruwan kasar za su halarci wannan gasa. An kasa wadanda za su shiga cikin gasar daidai da shekarunsu. 605296




captcha