Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na iidr an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a birnin Manchester na kasar Birtaniya, da zai yi dubi kan tafsirin surat waki'a da kuma dalilab safkar ayoyinta. Rahoton ya kara da cewa babbar manufar gudanar da zaman taro ita ce bayani kan hikimomin da ke tatter da ayoyin surar, da kuma wa'azin da Allah madaukakin sarki ya yi a ciki, day a hada da gargadi da kuma kwadaitarwa ga muminai. 604798