IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kur'ani Da Nahajul Balaga Ta Kasa

16:40 - June 29, 2010
Lambar Labari: 1948398
Bangaren harkokin kur'ani: a ranar ashirin da biyu ga watan Shaharivar na wannan shekara ne za a gudanar da gasar karatun kur'ani da Nahajul Balaga a fadin jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da halartar wadanda suka yi fice ta fuskar karatun kur'ani.

Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta watsa rahoton cewa a ranar ashirin da biyu ga watan Shaharivar na wannan shekara ne za a gudanar da gasar karatun kur'ani da Nahajul Balaga a fadin jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da halartar wadanda suka yi fice ta fuskar karatun kur'ani. Mu'assisar da ke kula da harkokin kur'ani ta ke shaidawa al'umma da duk mai bukata labarin fara gasar karatun kur'ani da harda da kuma ta Nahajul Balaga a ranar ashirin da biyu ga watan Shahrivar na wannan shekara na hijira shamsiya kuma tare da hadin guiwar ma'aiaktar harkokin al'adu ta Musulunci kuma gasar za ta kumshi bangarori biyu na mata da maza ba tare da la'akari da wasu shekaru na musamman ba.





605626
captcha