Bangaren al'ada da fasaha; a garin Lazkiya na kasar Suriya an gudanar da bincike kan tarihin baje koli a Iran kafi da kuma bayan Musulunci kuma an gudanar da hakan ne a wani zama da cibiyar al'adu ta Iran ta shirya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta da ke hukumar kula da al'adu da kusanci a tsakanin kasashen musulmi da musulmin duniya ta watsa rahoton cewa: a garin Lazkiya na kasar Suriya an gudanar da bincike kan tarihin baje koli a Iran kafi da kuma bayan Musulunci kuma an gudanar da hakan ne a wani zama da cibiyar al'adu ta Iran ta shirya. Said Ali Huseini shugaban cibiyar al'adu ta Iran a Lazkiya na kasar Suriya a cikin wani jawabi day a gabatar a gaban masu kula da al'adu da malaman jami'a ya bayyana muhimmancin wannan bincike da alfanon da ke tattare da shi.
605489