Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Brnama an bayyana cewa, za a fara gudanar da wani zama na makaranta kur'ani mai tsarki a birnin na lardin Sabah a kasar Malazia, wanda zai samu halartar makaranta kur'ani daga ko'ina cikin kasar. Cibiyar kula da harkokin kur'ani ta lardin ce za ta dauki nauyin shirya zaman taron, wanda irinsa na hamsin da uku da za a gudanar a kasar, kamar yadda aka taba gudanar da irinsa a lardin a cikin shekarun 1989 da kuma 2000. Yanzu haka dai cibiyo da kungiyon na karatun kur'ani na kasar sun fara shirin halartar taron. 606498