Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na cba ya habarta cewa, taron harkokin tattalin artzikin kasashen duniya zai yi dubi kan irin rawar da tattalin arziki irin na musulunci zai iya takawa wajen warware matsalolin tattalin arzikin duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai mayar da hanakali kan muhimman batutuwa da suke ci ma duniya tuwo a kawarya, tare da yin koyi da wasu daga cikin hanyoyin da tattalin arzikin musulunci ya dogara da su, domin shawo kan matsalar tattalin arzikin duniya. 606360