Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar sharq alausat an bayyana cewa, fitattun mutanen da suka shahara wajen rubutun kur'ani a duniya za su gudanar da wani zama na musamman a birnin Madina mai alfarma a cikin shekara mai kamawa. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa da suka shafi rubutun kur'ani ta hanyoyi na zamani, da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa wajen kara kyatata rubutun kur'ani mai tsarli. 606343