IQNA

Za A Bude Wata Cibiyar Horar Da Malamai A Kasar Mali

19:05 - June 30, 2010
Lambar Labari: 1949106
Bangaren kasa da kasa; Za a bude wata babbar cibiyar horar da malaman musulunci a birnin Bamako na kasar Mali a cikin wannan wata da muke ciki, da nufin kara wayar da kan malaman addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada labarai da hulda da jama'a na kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu ta kasashen musulmi ISESCO ya habarta a shafinsa na yanar gizo cewa, za a bude wata babbar cibiyar horar da malaman musulunci a birnin Bamako na kasar Mali a cikin wannan wata da muke ciki, da nufin kara wayar da kan malaman addini. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kungiya ita ce za ta dauki nauyin bude wannan cibiya, gami da taimakon kasashen da suke cikin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, bisa la'akari da matsayin da kasar Mali take da shi a bangaren raya ilmin addinin musulunci. 606170


captcha