Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ya yi da mataimakin shugaban jami'ar Almostafa Mehdi Mehr ya bayyana cewa, malaman addinin musulunci a kasar Iraki da suka shiga cikin wani shiri na bayar da horo sun karbi takardun shedar kammala samun horon a cikin wannan mako. Bayanin ya ci gaba da cewa malamin ya tabbatar da cewa dukkanin wadanda suka shiga cikin wannan shiri sun samu takardun shedar, kuma wannan shi ne Karon farko da aka gudanar da shirin, amma da yaradar Allah za a ci gaba da gudanar da shia acikin shekaru masu zuwa. 605793