Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alquran.in an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro da zai nazari kan harkokin tattalin arziki da kuma koyarwar kur'ani mai tsarki a kan hakan a jami'ar musulunci ta kasar India. Bayanin ya ci gaba da cewa taron zai samu halartar masana da kuma manazarta kan harkokin tattalin arziki na jami'oi daban-daban na kasar, inda za su mayar da hankali kan yadda za a iya yin amfani da mahagar kur'ani wajen bunkasa harkokin tattalin arziki. 606093